By Ishaq Dabai
Sanata Shehu Sani wanda yake wakilcin gundumar sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisa ta takwas daga 2015 zuwa 2019, daga karshe ya koma jam’iyyar PDP.
Sanata Sani wanda ya kasance Sanata a dandalin jam’iyyar APC a shekarar 2015 bai iya komawa majalisar dattawa ba a shekarar 2019 lokacin da ba a warware matsalolinsa da gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ba, kuma ya kasa samun tikitin jam’iyyar, hakan ce ta tilasta masa sauya sheka zuwa Jam’iyyar PRP wadda a karkashinta ya tsaya takara amma bai samu nasaraba inda ya fadi zabe.
Kwanan nan kawai ya watsar da jam’iyar PRP bayan haka ya ce yana tuntuba don sanin matakin da zai dauka na gaba, har zuwa ci gaban da ya samu wanda ya kafa tantinsa da PDP gabanin babban zaben 2023.
Ba a fayyace matsayin da zai tsaya takara ba a 2023 amma jita jita na nuni da cewa yana iya neman mukamin zartarwa a jihar ko watakila komawa majalisar dattawa.
Da yake tabbatar da ficewarsa, babban hadiminsa, Malam Suleiman Ahmed ya tabbatar da cewa “gaskiya ne sanata Shehu Sani ya gama shiga PDP amma bikin tarbar tasa da liyafar zata kasance cikin makonni biyu masu zuwa komai zai daidaita.”
Yace tsohon dan majalisar ya tabbatar da sauya shekarsa a ranar Alhamis, 16 ga Satumba, 2021 lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyar PDP a Kaduna.