By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yiwa Sarkin Jama’are Alhaji Ahmad Muhammadu Wabi III rasuwa bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
An ce Sarkin ya rasu ne da misalin karfe 12 na daren ranar Lahadi bayan shafe shekaru 50 yana mulki, ya bar mata biyu da ‘ya’ya 35.
Da yake bayyana rasuwar Sarkin Gadodamasun Jama’are, Alhaji Salleh Malla ya ce za a yi kewar marigayin sosai.
Ana sa ran gwamnatin jihar Bauchi za ta bayyana cikakken bayani game da yadda za’ayi jana’izar sa.