Mai Martaba Sarki Kontagora dake jihar Niger Alhaji Saidu Umaru Namaskar ya rasu.
Sarkin ya rasu ne yana da shekaru 84 a Duniya, bayan ya kwashe shekaru 47 a kan karagar Mulkin sarautar yankin.
Haryanzu dai ba’asami cikakken bayanai kan rasuwar shi ba, Amma jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Basaraken ya rasu ne a wani Asibiti dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya Isa Jihar Imo, domin Kaddamar da wasu aiyuka
Kazalika Haryanzu babu wata sanarwar da Masarautar ko iyalan Sarkin suka fitar a hukuman ce, Amma wata maji ta tabbatar da mutuwar Basaken.
Mutuwar basaraken na zuwa ne watanni Uku bayan Yan bindiga sun yi garkuwa da Dan shi, a wata gonar basaraken.
Tun a lokacin Dan Mamacin Alhaji Bashar Saidu Namaska ya na gonar Mahaifin shi ne, dake kan hanyar Zuru a karamar hukumar Kontagora lokacin da yan bindigan suka yi awon gaba dashi.
Kazalika a lokacin rahotanni sun nuna cewa, Yan bindigan sun hallaka wasu daga cikin mutanen da suke tare da shi, da kuma sace Shanu da damu.