By Abbas Yakubu Yaura
Sanata Enyinnaya Abaribe ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP.
Abaribe ya kuma ajiye mukaminsa na shugaban marasa rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar.
Idan zaku iya tuna cewa Abaribe wanda ya kasance dan takarar gwamnan Abia, ya fice daga zaben fidda gwani na gwamnan PDP a ranar Talata.
Ya tabbatar da sauya shekar sa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na yankin karamar hukumar Obingwa a jihar Abia da kuma shugaban majalisar dattawa a majalisar wakilai ta kasa, Ahmed Lawan.
Abaribe ya bayar da cewa ‘rashin gaskiya, da kuma shakku wajen yanke hukunci a matsayin dalilan sa ficewa daga jam’iyyar PDP.
Wannan ci gaban ya samo asali ne sakamakon rashin kunya da nuna rashin amincewa da hukuncin da jam’iyyar ta yanke, da kuma bayan shawarwarin da ya kamata a yi da mazaba na.” Ya kara da cewa.
Wasikar da ya rubuta wa Sanata Ahmed Lawan an karanta a wani bangare cewa, “Wannan don sanar da kai da abokan aiki na a Majalisar Dattawa cewa na yi murabus daga jam’iyyar PDP a hukumance ta hanyar mazabar ta.
“Wannan kuma yana nufin nayi murabus daga matsayin (Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa).
“Ina so in gode muku da abokan aiki na a cikin shugabancin Majalisar Dattawa saboda kyakkyawar dangantakar da muka yi a lokacin da nake Shugaban marasa rinjaye.”