Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da hafsoshin tsaro a fadar Shugaban kasa dake Abuja.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya taron ne, domin jin bayanai kan halin da ake ciki a kan fannin tsaron kasar nan.
A yan makokwannin nan dai, rundunonin tsaron, sun kara kaimi wurin yakar matsalar tsaro, da kuma Yan bindiga a fadin Nigeria.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dangantaka tai tsami tsakanin Yan Fim, da hukumar tace fina-finai
Daga cikin mahalarta taron akwai Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbanjo, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, Mai bai wa Shugaban kasa Shawara akan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno, Shugaban rundunar tsaro na Kasa Janar Lucky Irabor.
Sauran sun hada da, Babban Hafsan sojin kasa Manjo janar Faruk Yahaya, Hafsan sojin sama Air Marshal Isiaka Amoo, da kuma Shugaban rundunar tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Bichi.
Kazalika sauran mahalarta taron akwai; Minsitan Tsaro Bashir Magashi, Ministan kula da harkokin kasashen waje Geoffrey Onyema, da kuma ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.
Comments 1