Daga: Abbas Yakubu Yaura
A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron kwamitin tsaro na kasa (NSC) a fadar shugaban kasa dake Abuja.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa taron dai shi ne karo na biyu tun bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ke Abuja, wanda ya kai ga sakin ‘yan tada kayar baya da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-abia-ta-rushe-majalisar-kwalejin-kimiyya-da-dakatar-da-gudanar-da-ayyukanta/
A taron da ke gudana a cikin zauren majalisar akwai sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro DSS, Yusuf Bichi; da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abu, da sauran manyan hafsoshin tsaro.
A Wani Labarin Kuma Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya bukaci jam’iyyar da ta hada kan Najeriya, ta kuma mai da ita abin alfahari ga bakar fata.
Shettima ya kara da cewa, ba mahara ne suka lalata Roma ba, sai dai yadda Romawa suka yi kasa a gwiwa, inda ya ce lokaci ya yi da za a rera wakokin hadin kai da zaman lafiya da wadata da kwanciyar hankali don ganin Najeriya ta samu ci gaba.
Tsohon gwamnan jihar Borno ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja lokacin da Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya gabatar da shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a hukumance.
Ya ce, “A cikin makonni da watanni masu zuwa, dole ne mu shiga cikin ramuka, mu shiga lungu da sako don rera wakokin hadin kai, zaman lafiya, wadata da kwanciyar hankali.
“Bari mu hada kan kasar nan, mu maishe ta abin alfahari ga bakar fata.”
Shettima ya kuma bayyana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a matsayin jigon siyasa da halin rashin son kai.