- A yayin da ya rage kwanaki 5 shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika takardun mika mulki ga zababben shugaban kasa Tinubu.
- Wannan ya yi dai-dai da Dokar Zartaswa ta 14 wadda ta ba da umarnin.
- Mika bayanan shine domin gabatar da tsarin manufofin gwamnati mai zuwa.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, a Abuja, ya mika takardun mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
KARANTA WANNAN: Gobara Ta Tashi A Gidan Da Ganduje Zai Koma Bayan Rantsuwa
Buhari ya kuma mika sandar aiki tare da takardun a wajen babban kwamandan jamhuriyar tarayya na kasa kan Tinubu da kuma babban kwamandan oda na Neja kan mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a dakin taro na Banquet House dake Abuja,kamar yadda Punch ta rawaito.
Wannan ya yi dai-dai da Dokar Zartaswa ta 14 wadda ta ba da umarnin cewa majalisar mika mulki ta fitar da bayanan mika mulki da suka kunshi bayanai da dai sauransu domin gabatar da tsarin manufofin gwamnati mai zuwa.
A wani labarin kuma,‘Yan Majalisar Dokokin Bolivia Sun Baiwa Hammata Iska A Zauren Majalisa
Shugabannin kasar Bolivia sun yi Allah-wadai bayan da ‘yan majalisar da ke hamayya da juna suka yi taho-mu-gama a zauren majalisa.
Barkewar rigimar ta samo a saline yayin wata muhawara kan
makomar wani gwamna da ke daure da ‘yan adawa suka bayyana a matsayin fursunan siyasa.
An yi musayar naushe-naushe na mintuna da dama amma tashe-tashen hankula sun ƙare ba tare da munanan raunuka ba.