By Ishaq Dabai
Shugabancin jam’iyyar (APC) mai mulkin kasa ya sanar da dakatar da taron majalisar jihar Oyo dake gudana a halin yanzu saboda yin jabun takardu da aka shirya domin gudanar da aikin da sauran kura -kurai.
Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin tsare -tsare na musamman, Mai Mala Buni shine wanda ya ba da umarnin.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa Sanata John James Akpanudoedehe, da safiyar ranar Asabar,ya bayyana cewa dakatarwar ta zama dole don tabbatar da sahihancin tsarin da ke haifar da fitowar sabbin shugabanni a jihar Oyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa sanarwar ta tabbatar da cewa jam’iyyar APC karkashin gwamna Mai Mala Buni ba za ta lamunci aikata rashin da’a da yin magudi ba na kowane irin aiki.
“Ya zama tilas a dakatar da atisayen Majalisar Jihar dake gudana a Jihar Oyo saboda bayanai game da jabu na takardun da ake son gudanar da wannan aikin.
Sanarwar taci gaba da cewa “Shugaban na kasa, duk da haka ya umarci Kwamitin Majalissar Jihar Oyo daya koma Sakatariyar Kasa don ci gaba dayi masa bayani.”
Kazalika jam’iyar ta APC ta kuma tabbatar wa membobin jam’iyyar na daukar mataki da kuma yin adalci a kowane lokaci.