By Abbas Yakubu Yaura
Yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara gabatowa, wasu masu rike da mukaman siyasa na ci gaba da yin murabus daga gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya a jihar Gombe.
A kwanakin baya ne wasu mashawarta na musamman guda biyu a majalisar gwamna Hajiya Dijatu Bappa da Alhaji Garba Jijji suka yi murabus daga mukamansu.
Hakazalika, shugaban zartarwa na hukumar wasanni ta jihar Gombe Malam Hamza Adamu Soye a ranar Talata ya mika takardar murabus dinsa ga gwamnan.
A cikin wasikar murabus din mai kwanan wata 15 ga watan Fabrairu 2022 zuwa ga gwamnan,wanda wakilinmu ya samu kwafin, Soye ya ce murabus din nasa ya fara aiki nan take.
A wata hira ta wayar tarho, tsohon shugaban hukumar ya tabbatar wa wakilinmu wasikar amma bai yi karin haske kan dalilan daya sa ya sauka daga kan mukamin nasa ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ‘yan kwanakinnan dai ana kara samun murabus din masu rike da madafun iko a jihar ta Gombe duk da cewa basa bayyana dalilan su nayin hakan.