Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza mai shekaru 55 a duniya ya rasuwa, bayan da zuciyarsa ta buga.
A ranar asabar an kwantar da shi a asibiti bayan da ya fara jin jikinsa ba dadi, a ranar Litinin kuwa jikinsa ya dan yi sauki amma daga bisani sai jikin nasa ya kara tsanani wanda ta kai ga bugun zuciya.
Shugaban kasar yayi yunkurin sauka daga kagarar mulki a watan Agusta bayan da ya shafe shekaru 15 yana mulkin kasar.
A shekarar 2015 an samu tashe-tashen hankula bayan da bayyana ra’ayin sake zarcewa kan karagar mulkin kasar.
A lokuta mabambamta an sha yunkurin yi masa juyin mulki, amma ba a samu nasara ba wanda hakan ya jawo aka kama mutane da dama da suke da hannu a yunkurin wasu kuma suka tsere daga kasar baki daya.
Bayan da gwamnatin nasa tayi gyara a kundin tsarin mulkin kasar wanda ya bashi damar sake zarcewa, amma sai ya zabi ya sauka a watan Agusta shekarar nan.