Da dumi dumi: Shugaban Kasar Najeriya dole ya fito daga Kudu: Inji gwamnonin Kudu
Gwamnonin Kudu sun hada Kai kan cewa shugaban Kasar Najeriya dole sai ya fito daga kudu.
Sannan sun sanya 21 ga watan Satumba 2021 a matsayin ranar da zasu tabbatar da dokar kiwo a cikin Jahohin su.
KARANTA:-Gwamna Babagana Zulum ya maida yan gudun hijira na kananan hukumomi 5
Jagoran gwamnonin Kudu, Rotimi Akeredolu ya sanar da haka ga manema labarai a ranar Litini, bayan tattaunawar sirri da suka gabatar tsakanin gwamnonin a Alausa, Jahar Legas.