Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi hatsarin mota, in ji BBC a ranar Laraba.
Daily Post ta ruwaito cewa, Mai magana da yawun Zelensky, Sergii Nykyforov ya tabbatar da hakan a cikin wata gajeriyar sanarwa da ya fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Mahaifiyar Gwamnan Jam’iyyar APC Ta Rasu
Ya ce, “Likita ne ya duba shugaban, amma bai samu wani mummunan rauni ba”.
A cewar Nykyforov, jami’an tsaro na binciken dukkan al’amuran da suka shafi hatsarin mota. Bai bayar da wani karin bayani ba kan lamarin.
An bayyana cewa direban motar da ya yi karo da ayarin motocin fadar shugaban kasar ya yi ji rauni sosai a wurin da lamarin ya faru kuma an dauke shi an tafi da shi cikin motar daukar marasa lafiya.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Zelensky, ya ziyarci birnin Izyum da aka kwato, wani muhimmin cibiyar hada-hadar kayayyaki a arewa maso gabashin Ukraine, a ranar Laraba.
A WANI LABARIN KUMA: Yan sanda Sun Kaddamar Da Binciken Makashin Yar Shekara 14 A Filato
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta sha alwashin cafke wanda ya kashe wata yarinya ‘yar shekaru 14, Maryam Salisu, wadda aka kashe a ranar Talatar makon jiya a wajen kauyen Babale da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Batholome Onyeka, wanda ya samu wakilcin jami’in ‘yan sanda mai kula da reshen Nassarawa Gwong, SP Musa Hassan, ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci gidan iyalan marigayiyar