Da sanyin safiyar Talata ne dakarun Operation Forest Sanity suka kai samame, tare da ceto al’ummomin garin Kuriga da Manini da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kubutar da wasu mutane shida da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.
Dakarun bayan nasarar da suka samu a karshen mako, sun ci gaba da gudanar da aikin fatattakar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a sassan jihar.
A cewar rahoton da kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin cikin gida da tsaro Samuel Aruwan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce, “Sojoji sun farmaki tare da yin artabu da ‘yan bindiga a unguwar da ake zargin nan ne maboyar su. Bayan fafatawar Jami’an rundunar sojin sun ceto wasu mutane guda shida da aka yi garkuwa da su kuma aka boye su a wurin.
Sun ceci wadanda aka ceto din sune: Sahura Hamisu, Ramlatu Umar, Saudatu Ibrahim, Maryam Shittu, Fatima Shuaibu da Khadijah Mohammed (tare da jaririnta.
An jefi Tinubu da wasu Kalamai masu ɗaci kan ziyartar Obasanjo
Sanarwar ta bayyana cewa, an sada mutanen da aka ceto cikin koshin lafiya da iyalansu.
A cewar sanarwar, gwamnatin jihar Kaduna ta yaba da wannan rahoton, musamman ceto Mutanen guda shida da aka yi garkuwa da su, tare da godiya da kuma yabawa sojoji, jami’an ‘yan sanda, jami’an leken asiri, ‘yan banga da sauran jami’an tsaro, bisa nasarar da aka samu na sake gudanar da ayyukan cikin nasara.
Gwamnatin jihar Kaduna, a cewar sanarwar, ta mika godiyarta ga babban hafsan sojin kasa, babban hafsan dakarun soji, hafsan hafsoshin sojan sama, babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya, da kuma babban darakta a ma’aikatun gwamnati, don ci gaba da kai hare-hare da jami’an su ke yi a yankunan da masu laifi ke zaune
Ta kuma ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da gudanar da ayyukan su a yankin baki daya da sauran wuraren a fadin jihar.