Rahoton da ya iske mu yanzu ya tabbatar da tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Korona.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito, ta ce wani makusancin tsohon gwamnan mai suna Akin Alabi ne ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan.
Bayanai na nuni da cewa, Mista Abiola Ajimobi ya mutu ne a bangaren kulawar gaggawa da ke wani asibiti a Jihar Legas, bayan da ya fuskanci matsaloli da suka danganci cutar sarƙe numfashi.
Ajimobi ya rasu yana da shekaru 70 a duniya.
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka dinga yaɗa labaran karya a kafafofin sada zumunta akan mutuwar Ajimobi.
Kafin rasuwarsa, tsohon gwamnan shin mataimakin shugaban Jam’iyar APC na kasa kafin kwamitin gudanarwa na jam’iyar ya rushe shugabannin a taron da aka gudanar yau a Abuja.