Wata tankar man fetur ta yi taho mu gama a mile 2, dake yankin Otto wharf, na jihar Legas a yammacin yau Talata.
A cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, hukumar ta bude shirinta na amsa kiran waya daga Al’uma.
Gobarar da ke ci sosai ta haifar da firgici a yankin yayin da aka ga jami’ai da mazauna wurin suna kokarin shawo kan wutar da take ci.
“Bayan isa wurin da jami’an bayar da agajin gaggawa na hukumar suka yi, an ci karo da gobara daga wata tankar mai da ganguna.
Ya kara da cewa masu ba da agajin gaggawa “a halin yanzu suna fafatawa da wutar don kashe ta”
“Har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan agaji da ceto a yankin.
“Jama’a su kauracewa kusantar duk wata mota mai kama da wannan, yayin da masu ababen hawa su kaurace wa yankin, in ji kakakin hukumar LASEMA, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu a wata sanarwa da ya fitar.
A wani labari kuma na daban.
Shirun ‘yan bindiga kan sauran wadanda harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su, ya ba ni tsoro — Inji Wani Dan Gwagwarmaya
Wani dan fafutuka Musa Abilewa ya damu da yadda ‘yan bindiga suka yi shiru tun bayan sakin mutane bakwai da harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su, inda kuma ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta shiga tsakani wajen sako sauran 42 da aka yi garkuwa da su.
Musa Abilewa, wani mai fafutukar kare hakkin jama’a kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, ya ce yana tsoron kada ‘yan fashin da ba su ce komai ba, kuma ba su nuna wani faifan bidiyo na sauran wadanda akai garkuwa da su ba, tun bayan sakin wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su kuma aka ce wani gwamna ne ya taimaka musu.
“An shaida mana cewa wani gwamnan daya daga cikin jihohin Arewa, da ya fahimci cewa ‘yan asalin jiharsa bakwai na cikin wadanda abin ya shafa, ya taimaka wajen sakin ‘yan asalinsa cikin gaggawa, wanda hakan ya sa wadanda ba ‘yan asalin jihar nasa ba, suke cigaba da zama a hannun yan bindigar”.
Ya ce tun da gwamnonin da suka rage ba za su ji tausayin yadda za a sako ‘yan asalin nasu ba, to dole ne gwamnatin tarayya cikin gaggawa, kuma a matsayin daya daga cikin ‘yan Nijeriya, ta gaggauta yin ceto rayuwarsu.
Ya ce duk da cewa wadanda aka sako sun shaida cewa ba a azabtar da su ba, amma dajin ba wurin shakatawa ba ne.
A karshe ya kuma yi kira ga malaman addini, da su taimaka wajen karfafa addu’o’in neman taimakon Allah a kan wadanda abin ya shafa