Tsohon gwamnan jihar Ondo a jamhuriya ta biyu Bamidele Olumilua, ya rasu bayan da yayi ‘yar gajeriyar rashin lafiya.
Tsohon gwamnan ya rasuwa ne a safiyar ranar Alhamis din nan a garin Ikere dake jihar Ekiti.
Olumilua ya mulki jihar Ondo a jamhuriya ta biyu tsakanin shekara ta 1992 zuwa 1993 a karkashin inuwar Jam’iyyar SDP.
https://dimokuradiyya.com.ng/jihar-ondo-ta-amince-da-dokar-samar-da-rundunar-amotekun/
Yaron mamacin Muyiwa Olumilua, wanda shi ne kwamishinan yada labarai na jihar Ekiti shi ne ya bayyana rasuwar mahaifin nasa a safiyar Alhamis din nan.
Kwamishinan yace “Baba ya rasu da misalin karfe 3 na safiya, muna alfahari da shi da irin rayuwar da yayi da kuma irin tsarin da ya bari”.
Nan ba da jimawa ba za a bayyana yadda bikin birnesa zai kasance.