Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar ‘yan sanda reshen jihar Legas Alhaji Abubakar Tsav rasuwa. Hakan ya fito daga bakin Jami’insa na musamman Torkuma Uke wanda ya bayyana rasuwar da yammacin ranar Litinin din nan.
Uke yace marigayin ya rasu a cibiyar kula da marasa lafiya dake Makurdi.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-gwamnan-jihar-abia-ya-kamu-da-corona/
Kafin rasuwarsa Tsav ya rike mukamin shugaban hukumar karbar koke-koke na jihar Benuwe, sannan ya rike shugaban hukumar ‘yan sanda na jihar Legas.