Wani gini ya ruguje a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ginin mai hawa uku ya ruguje ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Mutum Ya Harbe Kaninsa Har Lahira, Yayin Gwajin Maganin Bingida
Ginin yana a Junction Adabor, a unguwar Ashi na garin Ibadan, dake karamar hukumar Ibadan ta Arewa.
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, dukiyoyin miliyoyin naira ne suka lalace a lokacin da ginin ya rufta amma ba a samu asarar rai ba a sanadiyar lamarin.
Majiyoyi sun ce, a jikin katafaren ginin a kwai kantin magani, babban kanti dak kuma wata coci.
Wani mazaunin garin Tunde Abulesowo wanda ya zanta da manema labarai ya bayyana cewa filin da ginin yake, an ta ba yin amfani da shi a matsayin makabarta kafin a sayar da shi.
Ya ce, “Lokacin da aka sayar da filin, an tono duk gawarwakin da ke cikin makabartar kafin a gina ginin, an gina ginin ne a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Akala.
“Gini ya kasance yana ba da alamar rushewa kafin daga baya ya rushe, kayayyakin milliyoyin naira da kadarori sun makale a cikin baraguzan ginin.
Kazalika DAILY POST ta nakarto cewa rugujewar ginin Ashi na zuwa ne ‘yan makonni bayan da wani gini ya ruguje a hanyar Awosika da ke cikin birnin.
A WANI LABARIN KUMA: Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Yankuna 12 A Jihar Edo
A kalla al’ummomi goma sha biyu galibinsu a kananan hukumomin Etsako ta tsakiya da Etsako ta gabas na jihar Edo ne ambaliyar ruwa ta mamaye yayin da kogin Neja ya cika makil
Daily Trust ta ruwaito cewa, al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Udaba-Ekphei, Anegbette, Ukpeko Orle, Ofukpo, Agbabu, Osomegbe, Udochi, Yelwa, Ake Island da Ifeku Islay.