Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wani ginin bene mai hawa biyu da ake tsaka da ginawa ya ruguje a unguwar Kubwa da ke Abuja, inda ma’aikata suka makale.
Jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) na gudanar da aikin ceto a lokacin da Daily Trust ta ziyarci wurin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Lauyan Dake Kare Hakkin Dan Adam Inibehe Effiong Ya Shaki Iskar ‘Yanci Daga Gidan Yari
Ba a dai san adadin mutanen da abin ya shafa ba, sai dai wani mazaunin garin ya ce an ceto wasu da suka jikkata kuma an kai su asibiti.
A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari
Rundunar sojin Najeriya a ranar Juma’a ta ce jami’an tsaro sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce tawagar jami’an ta hadin guiwa ce ta samu nasarar hakan, karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta daya (GOC) ta Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, tare da rakiyar tawagar kwamandoji da jami’an tsaro.
A cewar sa, yayin da suke gudanar da wani rangadi na duba aiki a jihar Kaduna a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, 2022, jami’an tsaro sun yi kokarin kubutar da wadanda abin ya shafa daga hannun gungun masu garkuwa da mutane a kauyen Manini da ke kan titin Pole Wire-Birnin Gwari. , Karamar Hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna.