By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun sare kan dan majalisar da ke wakiltar yankin gwamnan Anambra, Charles Soludo a majalisar.
An gano kan Hon Okechukwu Okoye a Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu inda aka rataye shi.
Gangar jikinsa bata nan da alamu sunyi amfani da karfi wajen yi masa kisan gilla inda suka tafi da ita.
A makon jiya ne aka yi garkuwa da dan majalisar tare da mutum daya a cikin motarsa kirar Toyota Sienna.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro ‘yan sandan daga baya sun kwato motar tare da tura jami’ai domin ceto dan majalisar.
Soludo ya yi fatan ceto dan majalisar sa yayin da yake gabatar da kasafin kudin Anambra da aka yi wa kwaskwarima ga ‘yan majalisar a ranar Juma’a.
Kakakin ‘yan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu ya tabbatar da cewa an kashe dan majalisar
Ya ce: “An tsinci kansa a kan titin Nnobi a yau (Asabar). Har yanzu dai babu wanda ake tuhuma a game da lamarin.”