A yau Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka kashe wani malamin addinin musuluncin nan mazaunin jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami-Gashua a Jajimaji, hedikwatar karamar hukumar Karasuwa ta jihar.
Kafar yada labarai ta Channles TV ta ruwaito cewa, malamin ya taso ne daga Gashua zuwa Kano a cikin wata motar safa inda maharan suka farmake shi.
Wasu mazauna Gashua sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe a Jajimaji mai tazarar kasa da kilomita 30 daga Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Tsaftace Fasfo, Hanyoyin Bayar Da Biza
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata tattaunawa da ya yi da wakilin majaiyar Jaridar Dimokuradiyya ta wayar tarho, ya ce an kama wadanda ake zargin da wannan aika dauke da bindigogi kirar AK-47 kuma suna hannun ‘yan sanda.
Gashua na daya daga cikin gari a jihar Yobe dake da dumbin yawan Al’uma da suka fi zaman lafiya, ko da a lokacin da ake fama da rikicin mayakan kungiyar Boko Haram.
A wani labarin kuma : Ƴan Sanda Sun Kai Sumame Kan Masu Garkuwa, Sun Ƙwato Bindigogi
Jami’an ‘yan sandan da ke aiki da rundunar ‘Operation Restore Peace’ sun tarwatsa wani sansanin masu garkuwa da mutane a dajin Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
A cewar ‘yan sandan, wani kazamin arangama da aka yi ya kai ga kama wani da ake zargin dan fashi da makami tare da kwato bindigogi biyu masu dauke da albarusai, kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito.