Daga: Abbas Yakubu Yaura
An hallaka wani jami’in dan sanda a jihar Ondo bayan farmakin da wasu ‘yan bindiga suka kai a ofishin ‘yan sanda na Okuta Elerinla.
Jaridar Dailys ta samu labarin cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki ofishin ne kuma suka kama jami’an da ke bakin aiki a ranar Litinin da misalin karfe 1:00 na safe.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/shugaba-buhari-ya-nada-baballe-ila-a-matsayin-mataimaki-na-musamman-kan-harkokin-majalissa/
Har yanzu dai ba a gano manufar ‘yan bindigar ba.
Yayin da ake ta harbe harbe mai tsanani, wani jami’in dan sanda mai suna Boluwaji Temenu, mai lamba AP. 207538 ya mutu a harin.
Da take tabbatar da harin, jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, SP Funmilayo Odunlami ta bayyana cewa jami’an ofishin sun samu nasarar dakile harin.
Odunlami ta kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda, Oyeyemi Oyediran ya umarci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar, SCID, da ta gaggauta daukar nauyin lamarin.