Wasu ‘yan bindiga da aka ce suna da yawa sun kai farmaki kauyen Kurmin Sata da ke da tazarar kilomita kadan daga Millennium City a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wasu a kalla 20 zuwa wani wuri da ba a san ko Ina ne ba.
A cewar daya daga cikin shugabannin Yan sakai JTF na yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da misalin karfe 12:16 na safiyar Asabar.
A cewarsa, a cikin mutane 20 da aka yi garkuwa da su da farko, mutane hudu sun tsere daga hannun masu garkuwar, wadanda suka mamaye al’umma da manyan makamai.
Ya bayyana cewa Mai anguwan kauyen da wasu masu rike da sarautar gargajiya, mata da yara na daga cikin wadanda aka sace.
Yayin da ‘yan bindigar ke ta harbe-harbe kan Mai Uwa da wabi, harsashi ya same Wani Mutum, ya kashe mutum shi,” inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai amsa kiran da ya yi na mayar da martani kan lamarin ba, kuma babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A wani labarin Kuma Makamancin wannan.
Yan bindiga Sun Kakaba Dokar Hana Noma A Zamfara, Sun Kashe Mutum 7
Akalla manoma bakwai ne aka kashe a gonakinsu a kauyen Faru da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara da sanyin safiyar Asabar.
Wani dan yankin mai suna Garba Abdullahi ya shaidawa Jaridar PUNCH cewa wadanda abin ya shafa na cikin gonakinsu ne domin girbe amfanin gona a lokacin da ‘yan bindigan suka kai musu hari suka kashe su.
Abdullahi ya bayyana cewa daya daga cikin ‘yan uwan sa Sani Akwala yana cikin manoman da ‘yan fashin suka kashe.
“Yayana, Sani Akwala na cikin wadanda wadannan ‘yan bindigar marasa Imani suka kashe ba tare da tausayi ba.”
Abdullahi ya ce ‘yan bindigar sun addabi kauyen tun farkon daminar bana.
Ya Kuma kara da cewa barayin sun sha alwashin cewa babu wani aikin noma da za a yi a yankin a lokacin daminar bana.
“‘Yan bindigar sun zagaya gonakin gonaki domin tabbatar da ana bin umarnin na su,” in ji Abdullahi.
Ya koka da cewa zai yi wuya manoma su yi noma a lokacin noman bana, yana mai kira ga hukumomin da suka dace da su gaggauta yin wani abu.
Ya bayyana fargabar cewa matukar ba a yi wani abu a kan lokaci ba, mutanen kauyen ba za su samu wani zabi illa yin hijira zuwa wasu wurare na daban ba.
“Muna shirin guduwa daga kauyen saboda kalubalen rashin tsaro da ake fama da shi domin mun fahimci cewa daga dukkan alamu ‘yan fashin ba za su bar mu mu yi noma a bana ba.”
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ci tura saboda ba a iya samunsa ta wayar tarho ba.