Masu garkuwa da mutanen da harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su sun saki uku daga cikin 43 da suka rage a hannunsu.
A ranar Lahadi ne ‘yan bindiga suka yi wa mutane 43 bulalai, inda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Mutanen ukun da aka saki maza biyu ne da mace daya, mai yiwuwa suna daga cikin wadanda aka yi musu mummunan dukan a ranar Lahadi.
Sai dai an sake su da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, ‘yan uwansu sun dauke su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ko da yake ba a tabbatar da hakan ba, har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto idan an biya kudin fansa, amma an samu labarin cewa har yanzu mutane 40 da yan bindigan ke tsare da su, na hannun masu garkuwa da mutane a dajin.
DSP Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna bai amsa kiran wayar da majiyar jaridar Dimokiradiyya tai masa ba domin tabbatar da hakan.
A wani labarin kuma na daban.
Kasar Indiya a ranar Litinin ta rantsar da sabuwar shugabar kasar Draupadi Murmu, wanda itace shugabar kasa ta farko data fito daga cikin kabilun kasar.
“Zaben da na yi ya tabbatar da cewa talakawa a kasar na iya yin mafarki da kuma cika su,” in ji ta bayan da ta yi rantsuwar kama aiki.
A Indiya, shugaban ya fi cika ayyukan wakilci, yayin da ikon gwamnati ya ta’allaka ne ga Firaminista.
Murmu, wacce ke cikin jam’iyyar Hindu mai kishin kasa ta BJP ta Firaminista Narendra Modi, ita ce mace ta biyu da ta taba rike mukamin.
‘Yan asalin ƙasar sun kasance kusan kashi 8.6 cikin ɗari na al’ummar Indiya kusan mutane biliyan 1.3 kuma galibi matalauta ne kuma marasa galihu.
Murmu wanda ta kasance tsohuwar malama ce, ta taba zama gwamnan yankin Jharkhand. (dpa/NAN