Majalisar dokokin jihar Imo, da yammacin ranar Litinin, ta tsige kakakinta, Kennedy Ibe. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Majalisar ta kuma zabi Emeka Nduka a matsayin sabon kakakinta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Mutane Uku Sun Rasa Ransu A Wani Kauye Da ke Jihar Benue
A yanzu majalisar dokokin jihar Imo ta sami shugabanni hudu cikin shekaru uku.
Tuni Magatakardan majalisar Chinelo Emeghara ya rantsar da Nduka a matsayin sabon shugaban Majalissar, wanda ke wakiltar mazabar jihar Ehime Mbano, sannan Amara Iwuanyanwu, ya zama mataimakin kakakin majalisar.
An zabi Ibe, wanda ke wakiltar mazabar jihar Obowo a matsayin kakakin majalisar a watan Nuwamba 2021, bayan an tsige Paul Emezim a matsayin shugaban majalisar.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Ihitte Uboma, Onyemaechi Njoku, ya shaida wa wakilin Jaridar Punch a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa ‘yan majalisar za su taimaka wa sabon shugaban majalisar wajen daidaita zaman majalisar.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yankewa Jgoran Masu Garkuwa Da Mutane Evans Mummunan Hukunci
A ranar Litinin ne aka yankewa wani mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, da wanda ake karansa, Victor Aduba, hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun hukunta manyan laifuka ta Ikeja da ke jihar Legas ne ya yanke hukuncin.