A kalla mutane 268 ne aka kwaso daga kasar China zuwa babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.
Jirgin da ya kwaso mutanen ya iso filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikwe a yammacin ranar Asabar din nan.
Kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter, shugabar ‘yan Najeriya mazauna ketare Abike Dabiri-Erewa, tace dole ne wanda aka kwasu ki killace kansu na tsawon mako biyu kamar yadda cibiyar dakile cututtuka ta kasa (NCDC) ta tanadar.
Wanda suka dawo din aun fuskacin matsaloli da dama wanda suka hada da wariyar launin fata daga hukumomin garin Guangzhou dake China.
https://dimokuradiyya.com.ng/covid19-najeriya-ta-kwaso-mutane-292-daga-saudi-arabia/
Da yawansu sun fuskanci cin zarafi ta hanyar koro su daga mazaunansu sakamakon kin bin dokar killace kai da gwamnatin Guangdong ta kafa sakamakon barkewar annobar sarke numfashi.
Wasu ‘yan Najeriya sun aike da faifain bidiyon wata mata tana shayar da jaririyarta akan titi.
Matar da ba a san kowace ba an ganta a cikin faifan bidiyon tana shayar da ‘yarta, babban yaron nata na kwance a kasa, ka rahotanni sun bayyana cewa an koreta ne daga mallahin dake take zaune.
Sai dai hukumar kasar China tace ta samarwa da ‘yan Najeriya 207 mazauni a otal kuma kyauta.
Gwamnatin tace ‘yan Najeriya na daga cikin mazauna ketare daga fito dasu domin yi musu gwaji da kuma killasu kamar yadda hukumar gudanarwa ta Guangzhou ta bayar.