Wasu ’yan takarar shugaban kasa guda bakwai a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi watsi da sunayen mutane biyar da aka mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari , kamar yadda gwamnonin Arewa suka yi tun da safiyar yau
‘Yan takarar dai sun nuna rashin amincewarsu da cewa ba a tuntube su ba kafin gwamnonin Arewan su kai ga wannan matakin.
Wadanda ke neman takarar akwai gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade; tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon Gwamna Rochas Okorocha da dan kasuwa Tein Jack-Rich.
Sun bayyana hakan ne a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar ranar Talata, inda suka nesanta kansu daga cikin jerin sunayen da gwamnonin APC dake Arewacin suka fitar .
Sunayen da aka mika wa Buhari sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.
A wani labarin Kuma na daban.
Jami’an tsaro sun hana ‘yan jaridar da aka amince da su don yada labaran taron musamman na jam’iyyar APC da ake gudanarwa a Abuja, inda jami’an tsaro suka hana su shiga filin taro na Eagle Square.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, ‘yan jarida da dama da suka taru a kofar shiga filin taron jami’an tsaron da suka yi ikirarin cewa suna aiki ne bisa umarnin da ke sama sun hana su shiga.
Jami’an tsaro sun yi ta harba barkonon tsohuwa kan ‘yan jaridan da suka tsaya tsayin daka kan hana su ko da da takardun shaidarsu.
A halin da ake ciki kuma, ‘yan takarar shugaban kasa bakwai da suke fafatawa a karkashin jam’iyyar (APC) sun yi watsi da sunayen mutane biyar da aka ce an mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya zabi dan takarar yarjejeniya.
Sun dage cewa ba wanda ya tuntube su kafin gwamnonin su kai ga yanke shawara.