By Abbas Yakubu Yaura
Wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja sun fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da karin wa’adin da aka yiwa wasu shugabannin kananan hukumomi shida da kansiloli.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa wa’adin shugabannin kananan hukumomin da kansiloli ya cika a ranar Alhamis kuma ya kamata a rantsar da sabbin jami’an da aka zaba a yau juma’a 20 ga watan Mayu.
Amma ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello, ya bayar da misali da hukuncin da kotu ta yanke tare da tsawaita wa’adin jami’an da shekara guda.
Karin wa’adin dai bai yiwa mazauna karamar hukumar Gwagwalada a safiyar Juma’a da dadiba inda suka fito kan tituna dan nuna rashin amincewa.
Mazauna yankin, wadanda suka tare hanyoyin tare da yin tashe-tashen hankula, suna neman a sauya matakin da aka dauka.
Lamarin dai, an tattaro cewa ya hana zirga-zirgar ababen hawa a yankin.
An dai gudanar da zaben kananan hukumomin birnin tarayya Abuja a ranar 12 ga watan Fabarairun 2022.