Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun Mista Segun Oladitan nan take.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Tesleem Igbalaye, ya sanyawa hannu a ranar Litinin din nan, ta kuma dakatar da wasu mambobin hukumar guda shida ba tare da bata lokaci ba.
KARANTA KUMA Zan Kori Sakatarorin Da Ka Nada A Ranar Litinin — Adeleke Ga Oyetola
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa An ce dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafe da dama da suka shafi rashin kudi, rashin aiki, rashin zuwa aiki da kuma cin zarafin ofishin shugaban hukumar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnan jihar Osun, Sanata Adeleke, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban OSIEC, Segun Oladitan da wasu mambobin hukumar nan take;
I. Mr. Yusuf Oyeniran
II. Alhaja Suibat Adubi
III. Prince Yinka Ajiboye
IV. Mrs. Abosede Omibeku
V. Mr. Dosu Gidigbi
VI. Mr. Wahab Adewoyin
“Wannan dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafe da dama da suka shafi almundahana, rashin aiki, rashin zuwa aiki da kuma cin zarafin ofishin shugaban hukumar.
“Har sakamakon binciken da ake yi wa shugaban da aka dakatar da mambobin hukumar, sakataren hukumar zai ci gaba da tafiyar da harkokin hukumar.”
A Wani Labarin Kuma FG Ta Ciyo Bashin Naira Tiriliyan 24 Daga CBN A Cikin Kasafin Kudi
Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 6.31 daga babban bankin Kasa CBN domin cigaban al’umma a cikin watanni 10.
Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta yo rancen kudi daga CBN daga Naira tiriliyan 17.46 a watan Disambar 2021 zuwa Naira tiriliyan 23.77 a watan Oktoban 2022.