By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni na nuni da cewa An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Hon Abok Ayuba Nuhu.
Inda tuni dai aka maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana ta karamar hukumar Bassa ta jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Mambobi 16 daga cikin 24 na majalisar ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi a zauren majalisar a ranar Alhamis.