By Abbas Yakubu Yaura
An sake samun fashewar wani abu a gidan gyaran hali na Abolongo dake garin Oyo a jihar Oyo a yammacin ranar Talata.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa fashewar, wacce ta afku a wajen ginin ba a samu asarar rai ba.
Wasu mazauna yankin na zargin cewa bam din yana daya daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka kai hari gidan yarin a ranar Juma’ar da ta gabata.inda ake zargin cewa bai fashe ba a lokacin harin na farko.
Jami’an tsaro sun kai ziyarar gani da ido domin tantance irin barnar da aka yi.
Idan zaku iya tunawa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a cibiyar a ranar Juma’a, inda suka kubutar da dukkan fursunonin dake cikin ginin.Maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 10 na dare.
Kakakin Hukumar Kula da gidan Gyaran Hali na Najeriya (NCS) a jihar, Olanrewaju Anjorin ya tabbatar da faruwar harin a ranar Asabar.
Comments 1