Hukumar DSS ta ci gaba da kakkabe abokan tattaunawar ‘yan bindigar, Tukur Mamu, tare da kama surukinsa, Abdullahi Mashi a daren Alhamis.
Majiyar Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa jami’an ‘yan sandan sirrin sun kuma ziyarci gidan surukin Mamu, Ibrahim Tinja,tare da kama shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Bindiga: Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara Ya Jagoranci Tawagar Jami’ai Masu Sintiri
An kama Mamu da wasu ‘yan uwansa hudu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ranar Laraba bayan an fitar da su daga kasar Masar bisa bukatar hukumomin leken asirin Najeriya.
An ce mawallafin yana tafiya Saudiyya ne don yin aikin hajji tare da matansa biyu, babban dansa, Faisal Mamu da kuma sirikinsa, Ibrahim Tinja.
Sai dai Daily Trust ta rawaito cewa yayin da aka sako matan Mamu, mawallafin, dansa da kuma sirikinsa suna tsare.
A wani labarin kuma,Da Dumi-duminsa: Mun Sami Kakin Sojoji, Kudade Masu Yawa A Gidan Tukur Mamu – DSS
Hukumar DSS ta ce ta kwato kayayyakin da suka hada da na sojoji, da wasu makudan kudade iri daban-daban a gidan mai shiga tsakani da ‘yan fashi, Tukur Mamu.
Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a wani bincike da Daily Trust ta gudanar kan wani samame da aka kai a kan gidan dake Kaduna da ofishin Mamu da safiyar yau Alhamis.