Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP,kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: PDP Ta Nada Wabara A Matsayin Sabon Shugaban BoT Na Jam’iyyar
Makinde ya zama sabon shugaban ne ‘yan mintoci kadan bayan tsohon shugaban, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yi murabus daga mukamin.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Chelsea Ta Tabbatar Da Graham Potter A Matsayin Sabon Kocita
Chelsea ta tabbatar da cewa, ta kammala daukar Graham Potter a matsayin sabon kocinta.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis da yamma, Blues ta bayyana cewa tsohon kocin Brighton ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar a Kunguyar.
Potter ya maye gurbin Thomas Tuchel wanda aka kora jiya jiya ta hannun mamallakin The Blues, Todd Boehly.
A kan komawa Chelsea, Potter ya ce: “Ina matukar alfahari da zama sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea FC, wannan babbar kungiyar kwallon kafa ce.