Gwamnatin tarayya a ranar Litinin din nan ta ce aikin jirgin kasa na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna zai dawo cikin wannan wata na Nuwamba.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayyana cewa Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ba da katin shaida na ma’aikatar sa a Abuja.
Ya ce an samar da isasshen tsaro domin tabbatar da lafiyar fasinjoji. Sai dai Ministan bai bayar da takamaiman ranar da za a ci gaba da aikin ba.
Sambo ya ce ma’aikatar ta koyi isassun darasi daga harin da aka kai a watan Maris wanda ya yi sanadin mutuwar fasinjoji da dama da ya kai ga dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A Wani Labarin Kuma Dalibai Sun Roki ASUU Kada Su Koma Yajin Aikin Sai Bayan Kammala Jarabawa
Daliban Jami’ar Tarayya ta Lokoja (FUL) a ranar Litinin din nan sun roki kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da kar ta koma yajin aikin sai bayan kammala jarrabawar zangon karatu na biyu.
Koke-koken daliban ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar ASUU ta ke gudanar da taron Majalisar a ranar Litinin din nan inda ake tattaunawa kan gazawar gwamnatin tarayya na gaza biyan albashin mambobinta bayan ta koma bakin aiki a ranar 14 ga watan Oktoba daga yajin aikin da ta yi na watanni 8.