Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC) ta ayyana lokacin soma gididdigar jama’a da gidaje na kasa daga ranar 29 ga Maris zuwa 1 ga watan Afrilun 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Shugaban NPC Nasir Kwarra ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a.
KU KARANTA KUMA Hukumar Kidayar Jama’a Zata Dauki Yan Najeriya Sama Da Miliyan Daya Aiki
“Har zuwa 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu, ma’aikatanmu za su kasance a fagen kirgar mutane,” in ji shi.
Kwarra ya kara da cewa kayayyakin fasahar da za a yi amfani da su za su iya kayyade gine-gine da filaye, da yin bayani dalla-dalla kamar wuri, shimfidar wurare da sauransu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Shugaban NPC, wanda ya ce hukumarsa za ta tabbatar da gudanar da sahihin aiki, ya kara da cewa, za a kuma kidaya wadanda ba ‘yan Najeriya ba muddin suna cikin kasar a lokacin atisayen.
A Wani Labarin Kuma Sultan Ya Jaddada Bayar Da Goyon Baya Ga Hukumar USAID Kan Ayyukan Da Take Aiwatarwa
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, ya ba da tabbacin bayar da cikakken goyon baya ga Hukumar USAID Breakthrough Action Nigeria da sauran hukumomin bayar da agaji da ke aiwatar da shirye-shirye daban-daban a jihar Sokoto.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a Sokoto ranar Juma’a a lokacin da tawagar USAID Partners Forum karkashin jagorancin Breakthrough Action suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa.