Kakakin jam’iyyar APC Mai mulki reshen jihar Delta, Ogheneluemu Sylvester Imonina, ya fice daga jam’iyyar.
Imonina ya mika takardar murabus din nasa ne a wata takarda mai taken ” Na yi murabus a matsayin Mamba na jam’iyyar APC, da mukamin mukaddashin sakataren yada labaran jam’iyyar a jiha Delta.
A cikin wasikar ya ce, “Ina so in yi amfani da wannan dama domin in mika godiyata ga shugabannin jam’iyar APC a mazabar ta Isoko Nation da ‘ya’yan jam’iyyar a fadin jihar, bisa goyon bayan da aka ba ni a lokacin da na ba da gudunmawata ga ci gabar jam’iyyar.
“Ga duk wanda ya goyi bayana, ina masa babban godiya.”
Sai dai ya kasa bayyana ko zai koma wata jam’iyya ne.