Daga: Abbas Yakubu Yaura
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Egor/Ikpoba-Okha dake jihar Edo, Hon. Jude Ise-Idehen, ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar ya rasu ne da safiyar Juma’a sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/majalisar-dokokin-bayelsa-ta-ki-amincewa-da-nadin-wata-kwamishiniya-da-gwamna-diri-ya-gabatar/
Kakakin Majalisar Wakilai, Rep Benjamin Kalu, ya tabbatar da mutuwar dan majalisar, amma ya ce har yanzu majalisar ba ta san musabbabin rasuwar ba.
A Wani Labarin Kuma Wata kungiya mai suna Gamayyar Maido da Muhalli Neja-Delta (NDERC) ta yabawa shedikwatar tsaro (DHQ) bisa sabon farmakin da ta kai kan barayin danyen mai da ke aiki a yankin.
Shugaban kungiyar, Mista Justice Eselomo, ya yi wannan batu ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Eselomo ya ce baya ga ceton kasar nan makudan kudade da za su shiga hannun masu aikata laifuka, ayyukan yaki da ta’addanci sun taimaka wajen ceton ‘flora da fauna’ da kuma lafiyar jama’a.
Ya ce hadin gwiwa tsakanin ma’aikata da sojojin ayyukan daban-daban a yankin ya ci gaba da samun sakamako mai kyau.
Kungiyar ta danganta sabon karfin da sojojin suka basu bayan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kudurin da babban hafsan tsaron kasar Janar Lucky Irabor ya yi na kawar da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.
“Mun tuna cewa CDS ya kai sakon sa na yaki da satar mai zuwa yankin Neja-Delta inda ya gana da Amayanabo na masarautar Nembe, Sarki Edmund Daukoru da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.
“Muna kuma yaba wa babban hafsan sojin ruwa, Vice Adm. Awwal Gambo da jami’an sojin ruwa bisa ga kokarin da suka yi.
“A cikin kwanaki 14 kacal, sojojin sun gano jimillar lita miliyan 3.07 na Man Fetur, lita miliyan 3.8 na danyen mai, lita 14,000 na Premium Motor Spirit da kuma lita 14,000 na kalanzir din Kerosine Dual Purpose a hannun barayin.
“Wannan zai ba da damar sanin irin abubuwan da kasar nan ke salwanta kafin a samu kwarin guiwar Sojojin Najeriya na bin barayin,” inji shi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Eselomo, ya nemi hadin kan al’ummar yankin domin baiwa sojojin kasar damar tunkarar matsalar da ta haifar da gurbacewar muhalli da kuma jefa lafiyar mutane cikin hadari.
“Yan baya za su yi mana hukunci a kan irin yanayin da muka bar wa yaran da ba a haifa ba.
Ya kara da cewa, “Lokaci ya yi da za mu sanya kasarmu da lafiyarmu sama da neman abubuwan baragurbi da ba bisa ka’ida ba wanda ya lalata al’ummominmu da kuma asarar rayuka,” in ji shi. (NAN)