By Abbas Yakubu Yaura
Wata kotun majistare dake zamanta a Nomansland, Kano, ta bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu’azu Magaji, a kan kudi naira miliyan 1.
Alkalin kotun, Mai shari’a Aminu Gabari, ya bayar da belinsa kan rashin lafiya.
Sai dai kotun ta bukaci wanda ake tuhuma daya mika fasfo dinsa, ya bayar da wadanda zasu tsaya masa har mutane 2, ciki har da hakimin kauyen Dan Sarauniya da kwamandan Hisbah daga Dawakin Tofa ko kuma babban Limamin.
An dage cigaba da sauraren karar har zuwa ranar 2 ga watan Maris.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kotun Majistare ta bayar da umarnin cigaba da tsare Magaji a gidan gyaran hali da ke jihar.
Magaji dai yana fuskantar tuhume-tuhume guda hudu da suka hada da bata suna, cin mutunci da gangan, munanan karya da kuma tada zaune tsaye ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
An kama Magaji ne a Abuja bayan ya fito a wani shirin gidan talabijin na Trust. Daga baya aka kai shi Kano da tsakar dare.