Kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jihar Legas, Idris Salako ya yi murabus.
Gbenga Omotoso, kwamishinan yada labarai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin din nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Omotoso ya ce Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya amince da murabus din.
Jami’in ya lura cewa ficewar Salako “wani share fage ne ga sake fasalin ma’aikatar da hukumominta”.
Karanta kuma: Rushewar Gini: Gwamnatin jihar Legas Ta Ayyana zaman Makoki na kwana 3
Sanwo-Olu ya gode masa bisa ayyukan da ya yi masa tare da yi masa fatan samun nasara a ayyukansa na gaba.
Gwamnan ya gargadi duk wadanda ke wannan fanni da su mutunta doka ko kuma su fuskanci illar rashin sanin makamar aiki.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, Salako ya bar mukamin ne bayan da wasu gine-gine suka ruguje a cibiyar kasuwancin Najeriya a cikin ‘yan shekarun nan.
A wani labarin kuma: Mutane Biyar Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota Da Ya Ritsa Da Su
Mutane 5 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da wata mota kirar jeep da wata babbar mota a Enugu-Agidi ta hanyar Awka zuwa Enugu Expressway a Anambra.
A cewar hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta tarayya, lamarin wanda ya afku a daren Lahadin nan, ya faru ne sakamakon gudu da kuma rashin tsaro.