By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas Sanata Ben Murray-Bruce, ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Madam Margaret Murray Bruce.
Ya ce mahaifiyarsa ta rasu ne da karfe 4:40 na safiyar ranar Talata.
Da yake bayyana rasuwar mahaifiyar tasa a shafinsa na Twitter, Sanatan ya ce ya samu nutsuwa da sanin cewa ya baiwa mahaifiyarsa dukkan kulawar da zai iya bayarwa a lokacin rayuwarta.
Ben Bruce ya rubuta, “Rayuwa. Lalle ne, kamar yashi a cikin iska, yau yana nan, gobe ya tafi. Mahaifiyata ta tafi. Ta rasu ne da karfe 4:40 na safiyar yau. Babban darajara mai ƙima, tsarin tallafi na, babban abokina, komai na—ta tafi.
“Ta’aziyyata ita ce, a rayuwarta, na bata, ba kawai komai ne kuɗi za su iya saya ba, amma mafi mahimmanci, na bata lokaci na, komai na.
“A lokuta da ba za a iya lissafawa ba, zan je gidanta in rungume ta in yi mata wasa ba gaira ba dalili sai soyayya, irin wanda ’ya’ya maza ne kawai suke tarayya da iyayensu. Ina sonki mama kuma ina kewarki. Wannan yana ciwo sosai. Naku har abada.”