By Abbas Yakubu Yaura
Bayan kwanaki biyu dayin garkuwa da mutane shida, a sashin ma’aikatan Jami’ar Abuja (UNIABUJA) da safiyar ranar Talata, masu garkuwar sun tuntubi iyalansu domin neman kudin fansa, kamar yadda jaridar Dimokuradiyya ta rawaito
Rahotanni sun bayyana cewa sun bukaci Naira miliyan 50 ga kowane daya daga cikin wadanda aka sace, wanda ya kai Naira miliyan 300 ga daukacin mutane shidan da aka sace.
An yi garkuwa da wani malami, da ‘ya’yansa biyu, da wasu mutane uku a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a harabar jami’ar a ranar talata .