By Abbas Yakubu Yaura
Ebelechukwu, uwargidan tsohon Gwamna Willie Obiano da matar marigayi Ikemba Nnewi, Bianca Ojukwu, sun yi wani gangamin musayar kalamai a wajen bikin nadin Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan Anambra a ranar Alhamis.
Wasan kwaikwayon ya faru ne a lokacin da matar Obiano ta isa bikin bayan da Soludo da mataimakinsa, Onyekachi Ibezim, suka karbi rantsuwa daga babban alkalin kotun, Mai shari’a Onochie Anyachebelu ya rantsar da shi da misalin karfe 10:55 na safe.
DUBA WANNAN LABARIN: Hukumar NDLEA Ta Kama Masu Safarar Miyagun Kwayoyi 111 A Jihar Kaduna
Matar Obiano, wacce ke zaune kusa da Sanata Uche Ekwunife da kakakin majalisar Anambra Uche Okafor, ta tashi tsaye domin ta zauna da mijinta lokacin da rikicin ya faru.
A kan hanyarta ta zuwa inda Obiano ke zaune, ta ga matar Ojukwu ta yi ado da kyau ta zauna.
Da take fuskantar ta, matar Obiano ta ce: “Kin ce ba za mu zama Gwamna ba, ‘yar iska.”
A fusace Bianca ta amsa da sharara mata mari.
A wani mataki na ramuwar gayya, uwargidan Obiano ta rike gashin Bianca da riguna kafin jami’an tsaro da sauran manyan baki su yi katangar shiga tsakani, inda suka gargadi manema labarai da su kwashe kayan aikinsu cikin gaggawa.
Yayin da aka ci gaba da gwabzawa, Obiano, Soludo da Sanata Uche Ekwunife da dai sauransu sun yi mamaki.
Kafin uwargidan Obiano ta isa filin taron, jami’an tsaro sun hana ta shiga ta babbar kofar yayin da aka wareta ga Bishof domin shiga ta wannan hanya.
Ta sauko daga motarta ta fara buga kofar shiga inda ta umurci jami’an tsaro su bude mata.
Sai dai jami’an tsaron sun ki amincewa, inda suka ce suna aiki bisa umarni ne.
Bayan an tafka ta’asa, Obiano ya bar wurin nadin gwamnan nan da nan kafin jawabin Soludo tare da matarsa, ya nuna bacin rai.
Babu wani daga cikin jiga-jigan da suka halarci taron da ya so ya tattauna batun da manema labarai.
Sai dai wasu da suka mayar da martani kan lamarin bisa sharadin sakaya sunansu, sun zargi matar Obiano da laifin faruwar lamarin.