Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi; da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a birnin Landan.
Duk da cewa har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai game da taron har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, jaridar The PUNCH ta samu labarin cewa wani bangare ne na tattaunawar da ake yi gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ta Ayyana Yajin Aikin Sai Abunda Hali Yayi
Wike ya halarci taron tare da abokansa da suka hada da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo; Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue; Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke da dai sauransu.
Wakilinmu ya tattaro cewa nan gaba a yau kuma za a yi ganawar Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a birnin Landan.
Kafin taron na yau a birnin Landan, jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa ana kara samun fargaba a jam’iyyar PDP na cewa rikicin da ke tsakanin Atiku da Wike na iya shafar damar sa a zaben shugaban kasa na 2023.
Shugabannin jam’iyyar, wadanda suka zanta da PUNCH, a wata tattaunawa daban-daban a ranar Laraba, sun nuna damuwarsu kan yadda dangantaka tsakanin Wike da jiga-jigan jam’iyyar APC ke kara tasiri inda suka bayyana ci gaban a matsayin abin damuwa.
Manyan ‘ya’yan jam’iyyar sun nuna damuwa musamman kan ganawar da Wike da wasu gwamnonin PDP biyu suka yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a Landan ranar Litinin.
Dattawan jam’iyyar na fargabar cewa ayyukan Wike da gwamnonin jihohin Oyo da Benue, Seyi Makinde da Samuel Ortom, na iya yin illa ga damar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa ganawar da aka yi ranar Talata tsakanin Wike da Tinubu a kasar Birtaniya ta mamaye magana a tsakanin shugabannin jam’iyyar PDP a ranar Laraba.
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa ya gana da ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a fadin jihohi 36 na tarayya a hedikwatarta ta Wadata Plaza da ke Wuse, Abuja, ranar Laraba.
Taron dai ya samu halartar daukacin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP in ban da gwamnan jihar Oyo, wanda a halin yanzu baya kasar.
A wani labarin kuma Wata Budurwa Ta Cefanar Da Santalelan Jaririnta Kan Zunzurutun Kudi 600,000
Wata uwa ‘yar shekara 23 mai suna Mary Olatayo ta sayar da jaririnta dan kimanin sati uku da haihuwa a kan kudi naira 600,000, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta bayyana.
‘Yan sanda sun cafke Olatayo ne a ranar 18 ga watan Agusta, biyo bayan korafin da mahaifin jaririn ya yi a hedikwatar ‘yan sandan Mowe dake jihar Ogun.