By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga a ranar Litinin da yamma sun kashe wani jami’in soji a lokacin da suka kai wa wasu sojoji hari a Awo Mmamma dake karamar hukumar Oru ta Gabas a jihar Imo.
A wani mataki na ramuwar gayya ne wasu sojoji suka taru jami’an su inda suka mamaye garin tare da kona otal da motoci da gidaje da shaguna dake yankin.
Lamarin daya faru a mahadar Ishieke dake yankin ya haifar da firgici a cikin al’umma.inda ‘yan asalin yankin da dama sun gudu yayin da sojoji suka mamaye al’ummar.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Dimokuradiyya cewa, “wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu sojoji a mahadar Ishieke dake Awo Mmamma inda suka kashe daya daga cikinsu. Sun zarce zuwa Ihiala ta jihar Anambra. Daga baya sojoji sun mamaye yankin inda suka yi barna a yankin inda suka kona otal da motoci da gidaje da rumfunan sayar da ruwa”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, bai amsa sakon karta kwana da wakilinmu ya aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Har ila yau, mai magana da yawun rundunar ta 34 Artillery Brigade Command dake Owerri, Sunday Akuga, bai amsa kiran da akayi masa ba.