Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun, ta dakatar da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Dotun Babayemi.
Shugabannin mazabar Otun Balogun 2, dake karamar hukumar Ayedaade ne suka dakatar da Babayemi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Komai Yayi Wahala A karkashin Mulkin APC – Makarfi
A halin yanzu dai Babayemi na neman adalci dangane da cece-kucen da ke tattare da dan takarar gwamna na gaskiya na jam’iyyar a jihar.
Ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na zaben fidda gwani na gwamna, yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Sanata Ademola Adeleke a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Shi kuwa Babayemi, an kori shi daga PDP ne saboda zargin da ake masa na cin amanar jam’iyyar.
Shugabannin gundumar Otun Balogun 2 ne suka bayyana hakan a lokacin da suke ganawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta jihar da ke Osogbo a ranar Juma’a.
Da yake karanta jawabin a madadin kungiyar EXCO, sakataren gundumar Ogunleye Bukayo, ya ce an kori dan takarar gwamnan na bangaren ne sakamakon karar da wasu ‘yan jam’iyyar suka shigar a kansa.
“Kwamitin zartarwa na jam’iyyar a taronsa na ranar 20 ga watan Yuli, 2022, ya karbi rahoton kwamitin ladabtarwa, kuma bayan nazari mai zurfi ya amince da rahoton kwamitin ladabtarwar.”
“Kwamitin zartarwa na jam’iyyar wanda yake gudanar da ayyukan da sashi na 57(2) da 59 (1) (g) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ya cire tare da fitar da Prince Dotun Babayemi daga jam’iyyar PDP Don haka ya daina zama dan PDP daga yanzu,” in ji Ogunleye.
A wani labarin kuma, Tinubu Ya Jajantawa Gwamnatin Kano Kan Rugujewar Ginin Kasuwar Kantin Kwari
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan rayukan da aka rasa a lokacin da wani bene mai hawa uku ya ruguje a kasuwar Kanti Kwari da ke birnin jihar.
Tinubu a cikin wata wasika ta sirri da ya rubuta wa Gwamna Ganduje mai dauke da kwanan wata 31 ga watan Agusta, 2022 ya bayyana matukar bakin ciki da juyayinsa kan wannan mummunan lamari mara dadi.