A ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba, 2022, jam’iyyar PDP ta bayyana tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara a matsayin shugaban riko na kwamitin amintattu na jam’iyyar bayan murabus din Walid Jibrin.
An kuma nada shi a matsayin mai baiwa shugaban jam’iyyar PDP na kasa shawara kan harkokin siyasa, Dr. Iyorchia Ayu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yakamata INEC Ta Tuhumi Lawan, Akpabio Da Laifin Karya Dokar Zabe – Rafsanjani
Wabara, wanda kafin yanzu shi ne Sakataren PDP BoT, za a nada shi a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP.
Idan dai za a iya tunawa, a safiyar yau ne Jibrin ya sanar da murabus din sa a taron jam’iyyar PDP BoT, a sakatariyar jam’iyyar adawa ta kasa dake Abuja.
“Na sauka ne daga matsayin shugaban BoT. Na sauka ne domin saukakaw dukkan mu,” inji shi.
Jibrin ya rike mukamin na tsawon shekaru shida bayan ya karbi mulki daga hannun Haliru Bello da aka tsige a shekarar 2016.
Murabus din dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake neman karin wasu shugabannin kudancin kasar nan su bayyana a cikin shugabannin jam’iyyar gabanin zaben 2023.
A daya bangaren kuma akwai sharadin goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam’iyyar na kudancin kasar suka yi.
A halin da ake ciki, wata majiya ta ce gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, shi ma zai yi murabus nan ba da jimawa ba a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin PDP, in ji majiyar.
A wani labarin kuma, Da Dumi-dumi: Majalisar Dokokin Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye Da Mataimakinsa
‘Yan majalisar dokokin jihar Neja sun tsige shugaban masu rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye da kuma bulaliyar majalissar dokokin jihar.
‘Yan majalisar kuma sun zabi wadanda za su gaje su nan take.