By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun tabbatar da cewa Oba Lamidi Adeyemi na III, Alaafin na Oyo, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.
Har yanzu babu cikakken bayani game da rasuwarsa, amma Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa fitaccen sarkin Yarbawa ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti da yammacin ranar Juma’a.
DUBA WANNAN LABARIN: Harin Jiragen Sama: NAF Tayi Luguden Wuta Tare Da Tarwatsa Sansanin ‘Yan Bindiga A Jihar Taraba
An ce basaraken ya je a duba lafiyarsa ta yau da kullun inda ajali ya cimma sa “.
A cewar wata majiya, an gaggauta dauke gawarsa zuwa garin Oyo da sanyin safiyar Asabar dan fara gudanar da shirye-shirye jana’izar sa.
An ruwaito cewa dansa na farko, Prince ‘Tunde Adeyemi da sauran ‘yan uwansa, sun karbe shi ne a unguwar Idi-Igba da ke garin.
Ana sa ran shugaban Oyomesi, Basorun na Oyo, Chief Yusuf Akinade Ayoola, zai karbi ragamar harkokin fadar har sai an nada sabon Alaafin.
A safiyar ranar Asabar ne ake sa ran Basorun zai yi wa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde bayani a hukumance.
Tafiyar Oba Adeyemi ya zama basarake na uku, adadin manyan sarakunan Oyo da suka shiga sahun kakanninsu a wata biyar da suka wuce. Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi ya rasu ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2021 yayin da Olubadan Saliu Adetunji ya rasu a ranar 2 ga watan Janairu, 2022.
Comments 2