Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP a hukumance.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wannan dai na zuwa ne bayan watanni uku da komawar Shekarau daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.
Shekarau ya bayyana haka ne a ranar Litinin din nan a gidansa da ke Mundubawa a Kano.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, da sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP ne suka tarbe shi a hukumance.
Karanta: kuma: Batun Ficewar Sanata Shekarau Daga NNPP Zuwa PDP Shifcin Gizo ne
Shekarau ya kuma ce ya rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) takardar shelanta janyewa daga takarar sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar NNPP.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Sauran jiga-jigan PDP da suka halarci taron sun hada da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa; gwamnonin Sokoto da Taraba, Aminu Waziri Tambuwal da Darius Ishaku.
Sauran sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, shugaban shugaban kwamitin amintattu BOT na jam’iyyar, tsoffin gwamnonin Jigawa (Saminu Turaki da Sule Lamido), Sokoto (Attahiru Bafarawa), Kaduna (Ahmed Makarfi), Adamawa (Boni Haruna), da dai sauransu. .
A wani labarin kuma: Ogun: Jam’iyyar APC Za Ta Dakatar Da Shugaban Jam’iyyar Da Wasu
Jam’iyyar APC reshen jihar Ogun, ta kammala shirin dakatar da Cif Derin Adebiyi, shugaban jam’iyyar a jihar da tsohon Gwamna Ibikunle Amosun ke marawa baya, kan wasu ayyukan da suka saba wa jam’iyyar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wasu majiyoyi da dama a sakatariyar jam’iyyar APC sun tabbatar da cewa an gano Adebiyi da wasu ‘yan jam’iyyar masu biyayya ga Amosun sun kafa jerin sunayen wakilan da suka halarci zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC a jihar, kamar yadda jaridar DAILY POST ta rawaito.