By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Alhamis.
Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da ya yi da daukacin masu rike da mukaman siyasa a zauren majalisar gwamnati a daren ranar Talata.
A cewarsa, babban makasudin ziyarar shi ne jajantawa da kuma yin ta’aziyya ga gwamnatinsa kan hare-haren ta’addanci da aka kai a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum inda aka kashe mutane 58 a yankunan.
Ya ce an shirya komai don ganin an tarbe shugaban cikin nasara.
“Ina so in sanar da daukacin al’ummar jihar Zamfara cewa Kwamandan na Tarayyar Najeriya zai zo Zamfara ranar Alhamis musamman domin ziyarar jajantawa kan harin ‘yan fashi suka kai kwanannan a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar.” Yace.
Gwamna Matawalle ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda yayin ziyarar da shugaban zai kai.