By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan ya rasu.
Kamfanin dillancin labarai na kasar WAM ne ya ruwaito haka a safiyar ranar Juma’a.
Da Dumi-dumi: Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kano Ya Fice Daga Jam’iyyar APC
“Ma’aikatar Harkokin Shugaban Kasa ta yi ta’aziyya ga mutanen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma duniyar Musulunci… a kan rasuwar Sheikh Khalifa bin Zayed Al-Nahyan a ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu,” in ji WAM.
Da yake tsokaci kan wannan mummunan labari, Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya ce Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi rashin da da shugaba adali.
Ma’aikatar ta ba da sanarwar kwanaki 40 na zaman makoki tare da yin kasa kasa da tutoci a daga ranar Juma’a.
Sannan ta dakatar da ayyukan gwamnati da masu zaman kansu na kwanaki uku na farkon zaman makoki.
Sheikh Khalifa ya zama shugaban UAE na biyu a watan Nuwamba shekarar 2004.
Ya gaji mahaifinsa a matsayin sarkin Abu Dhabi na goma 16.